Hanyar samun kudi a Internet


yanda ake samun kudi a internet
Kashi na biyu

 masu saurare barkan mu da saduwa a wannan lokaci. Idan baku manta ba a shirin da ya gabata munyi alkawarin kawo muku cikakken bayani akan hanyoyin nan huɗu da ake samun kudi a internet. wanda hakan zai baka/ki Samar samun kudi a gida kuma a kowane lokaci.                                                                   Idan zaku tuna hanya ta farko da muka ambata itace;.                

 BUƊE SHAFIN YANAR GIZO

 Shafin yanar gizo (website) damace da ake samun kudi da ita ta kafar sadarwa ta intanet, Wadda kuma take tashe a halin yanzu.                                                    saidai yana da kyau mai sauraro ya sani, ba kawai da zarar ka bude shafin za a cigaba da turo ma ka/ki kudi ba, da akwai wasu yan ka'idodi da za abi tukuna. da zarar ka cika wadannan ka'idodi to zasu rika biyan ka .                                             kuma ku sani su Turawa ba kamar yan Afirka ba, sunfi mu  kokari wajan ganin cewa da lokaci yayi su biya ka kudin ka ba tare da wata titjiya ba.                                                        Daga cikin nau-ukan shafukan da ake dasu akwai; 

1- BUSINESS WEBSITE 

2- BLOGS 3 E-COMMERCE

 4- PORTFOLIOS 

5- EVENT WEBSITE 

6- ONLINE FORUM 

7- PERSONAL WEBSITE 

8- MEMBERSHIP WEBSITE 

9- NON-PROFIT WEBSITE 

10- INFORMATIVE WEBSITES 

zaka/ki iya buɗe Kowane daga wadannan nau'ikan shafukan da muka zayyano domin ka/ki rika samun kudi. da fatan zaku kara zirfafa bincike don kuma ku amfana da wannan dama, da al'umma ke ta cin gajiya a fadin duniya.                                                wani abun burge wa anan shine ba wani mawuyacin aiki ne akeyi ba illa kawai zasu rinka saka yan tallace tallace ne a shafin, wanda zasu rika biyan mai shafin .          wannan shine kawai bukatar su, sai su kuma suna biyan ka . 

 zan ɗan dakata anan. sai a karo na gaba zamu dasa akan;-                     Referral (jagora)

Da fatan zaku kasace Tare Da wannan shafi namu mai albarka. Mun gode

Comments

Popular posts from this blog

MU KOYI COMPUTER

BASIC COMPUTER SYSTEM ll

HAUSA WEB SERVER