BASIC COMPUTER SYSTEM ll
software
sune tsare-tsare ne (programme) wanda keba computer damar fahimtar abinda mai amfani da ita yake so ta aiwatar. Misali Windows, spreadsheet, Ms software etc.
Human ware:
human ware shine mai sarrafa computer.
SYSTEM UNIT
computer na kunshe da sassa (unit) guda hudu;
1. sashen shigar da bayanai (input unit),
2. sashin fitar da bayanai (output unit),
3. sashin masarrafi (control unit), da kuma
4. sashen mataskaci/ma'adana ( memory).
INPUT UNIT;
wannan sashe ya kunshi dukan bangarorin computer wadanda ake shigar da bayanai ta hanyar su. Duk bayanan da za a shigar to sune ake aiki dasu. eg keyboard, scanner, mic, light pen.
OUTPUT UNIT;
shi kuma wannan sashe ya kunshi dukan bangarorin da computer ke fitar bayanai ta hanyar su kamar speaker, monitor, printer etc.
CONTROL UNIT:
shi control unit shine sashen da ke sarrafa computer. wannan ofsashe shike ɗauke da alhakin du wani shigi da fici na computer. haka zalika kowane bangaren na computer gurin sa yake karbar ummarni.
Computer storage (tumbin computer);
Shi rumbun computer sashe ne na computer wanda yake ajiye bayanai kama daga rubututtuka, sati, hotuna da bidiyoyi. Computer storage yakasu kaso biyu, na farko shine primary storage, na biyu kuma shine secondary storage.
∆ Primary storage rumbu ne wanda yake rike aiki da ake gudanarwa computer kafin ayi mashi azauni na dindindin (saving). Misali RAM ( Random Access
∆ Secondary storage shine rumbu wanda yake ajiye bayanai a mazauni na dindindin, wanda koda ka kashe computer idan ka sake kunna ta o wannan bayanai bazasu gogeba. Misalin su; hard disk drive, ploppy disk , Flash drive, SD card etc.


Comments
Post a Comment