MU KOYI COMPUTER
me ake nufi da na'ura mai ƙwaƙwalwa?
Na'ura mai ƙwaƙwalwa (computer) na nufin mashin mai amfani da wutar lantarki, wanda ke karbar danyun bayanai (data), ya sarrafa su izuwa sakamakon bayanan (information).
Computer nada saurin aiwatar da aiki, kuma tana da sauki koyo, haka zalika tana aiwatar da aiki mai kyau/inganci.
computer components. computer ta kunshi components guda Uku, gasu kamar haka;
Hardware, software da human ware. hardware sune ake amfani dasu wajen shigar da bayanai, fitar da bayanai ko ajiye bayanai.
1. Hardware shine bangarorin da suke a bayyane a zahiri, wadanda za a iya gani da ido kuma za'a iya taba su.
2. software sune tsare-tsare ne (programme) wanda keba computer damar fahimtar abinda mai amfani da ita yake so ta aiwatar. Misali Windows, spreadsheet, Ms software etc.
3. Human ware: human ware shine mai sarrafa computer.
SYSTEM UNIT
computer na kunshe da sassa (unit) guda hudu;
1¹ shigar da bayanai (input unit), sashin fitar da bayanai (output unit), sashin masarrafi (control unit), da kuma sashen matsakaici/ma'adana ( memory).
INPUT UNIT; wannan sashe ya kunshi dukan bangarorin computer wadanda ake shigar da bayanai ta hanyar su. Duk bayanan da za a shigar to sune ake aiki dasu. eg keyboard, scanner, mic, light pen.
OUTPUT UNIT; shi kuma wannan sashe ya kunshi dukan bangarorin da computer ke fitar bayanai ta hanyar su kamar speaker, monitor, printer etc.
CONTROL UNIT: shi control unit shine sashen da ke sarrafa computer. wannan sashe shike ɗauke da alhakin du wani shigi da fici na computer. haka zalika kowane bangaren na computer gurin sa yake karbar ummarni.
MEMORY: memory shine ma'adanar computer, wanda yake dauke da sassa Kamar haka; read only memory (ROM), da random Access memory (RAM).
Comments
Post a Comment