Fasahar sadarwa

Masu sauraren mu da biyan mu, barkan mu da sake saduwa a  wannan makala tamu mai taken                   (fasahar sadarwa).
Fasahar sadarwa

Kamar dai yanda aka sani fasahar sadarwa fage ne na Musamman da ake kira da  "communication technology"  a turance, wanda yake kunshe da sassa daban daban, kamar Injiniyanci (Engineering), tsare-tsare (programming), tsarin sarrafa bayanai ( Data management system), wadanda sune manyan bangarori a fasahar sadarwa 
( communication technology). 
 
Rabe-raben Fasahar sadarwa
Fasahar sadarwa ta karkasu izuwa kashi hudu;- 1. Wayar salula ( phone )
             2. Radiyo (Radio)
             3. Talabijin (Television)
             4. Internet ( yanar gizo)
Duka wadannan an samesu ta hanyar fasaha ta zamani ta na-ura Mai ƙwaƙwalwa Wato
" Computer" a turance.

Wayar salula ( phone), ɗaya ce daga cikin manyan fasahohi a bangarori na sadarwa, wadda take bada gagarumar gudummawa a fagage daban daban na rayuwar ɗan adam, kama daga ilimi, kasuwanci, zumunta, kimiyya dadai sauran su. An samu wannan fasaha ne ƙarni na 18 wadda Alexander Ya kirkira.
Ta fara ne daga 1G (first Generation), sanan aka samu cigaba inda 2G(second Generation)  tamaye gurbi, haka kuma 3G (third Generation) tazo da sabbin abubuwan da suka wuce na 2G,  yayinda 4G  itama tazo ta zarce 3G.

Radiyo (Radio) sanin kowa ne kafar sadarwa ta rediyo abuce mai dadadden tarihi a kasashen mu,  Wadda take bada gagarumar gudummawa wajen sadarwa. Kama daga ilimantawa, nishadantarwa, wayar da kan al'umma, dadai sauransu. 

An samu wannan fasaha ne a karshen karni na 18,Wadda Heinrich Hertz Ya kirkira. Wannan fasahar sadarwa ta kasu izuwa:-      AM, FM,da SW
                               AM, 
Tashoshi ne masu cin matsakaicin zango, kamar Gidan Radiyo Nigeria Kaduna, Gidan Radiyon jihar Katsina, gidan rediyon jihar Kano etc.
         FM, Tashoshi ne masu cin gajeren zango, misali; Sahara FM, premium FM, companion FM etc.
   SW, Tashoshi ne masu cin dogon zango.
Wanda aka fi sani da international broadcast, irin su BBC, VOA,Dw Radio etc.

Yanar Gizo (Internet)
wannan fasaha itace fasaha mafi girma da shahara a wannan lokacin. Wadda ta mamaye duk wata kafar sadarwa a halin yanzu. 

Ita kalmar internet,
Ma'anar ta shine inter networking. Wadda ta har haɗe gamayyar networks, haka kuma tana bada gagarumar gudummawa a kowane bangare na rayuwar ɗan adam, a wannan doron duniya. Misali, social media, kimiyya da fasaha, kasuwanci, ilimi,zirga zirga etc. Kafar sadarwa ta intanet abuce mai faɗin gaske wanda lokaci bazai bamu damar bayyana taba  a yanzu, amman zamu fadada muku bayanai a karo na gaba akan wannan kafar sadarwa tare da alfanonin dake cikin ta.

Kunci gaba da biyar mu                    domin samun                      bayanai na musamman                           bakan 
         fasaha da kere-kere. 
                Mun gode.

Comments

Popular posts from this blog

MU KOYI COMPUTER

BASIC COMPUTER SYSTEM ll

HAUSA WEB SERVER