#1 YANDA AKE SAMUN KUDI A YANAR GIZO ( INTERNET)

 



masu sauraren mu barkan mu da saduwa a wannan lokaci, kamar yadda aka sani cewa wannan shafi mai albarka an kirkira shine domin ilimantawa akan fasahar Da kere-kere

                Duba da cigaba da duniya ke samu ta fuskar technology wanda hakan ke kunshe da dimbin damarmakin da mafiya yawa jama'a Basu san da suba, wannan ba yana nufi basu da ilimi bane! a a saidai ace ba su maida hankali a bangaren ba. 

            Wannan dalilin ne yasa na rubuta wannan makala mai taken Hanyar Samun Kudi a Yanar Gizo watau "DIGITAL MARKETING" a turance.

Manufar mu anan itace haskaka ma masu bibiyan mu hanyar da zasu bi su iya samun yan kuɗaɗe da wayarsu ta hannu ( phone) ko na'ura mai ƙwaƙwalwa ( computer), maimakon lokacin da suke sharewa suna yin wasu abubuwa da muhimmancin su bai kai wannan ba, duk da cewa yanzu matasan sun zabura wajan neman nakansu, to wannan ma wata dama ce gare su da zasu rage ma kansu biyan kudin data daga alaihi su. 

Tambaya da da zamu amsa a wannan makala itace. 

MENENE DIGITAL MARKETING?

Digital marketing sabuwar fasaha ce da ake gudanar da kasuwanci ta kafar sadarwar internet (yanar gizo). ana amfani da na'ura mai ƙwaƙwalwa ko wayar hannu wajan aiwatar da ita. kuma ta kasance hanya mafi shahara wajen samun kudi a duniya halin yanzu. Abin tambaya shine dole ne sai kana da jali zaka iya wannan kasuwanci Koko?

amsa itace a'a Digital marketing Kamar gama garin kasuwanci ne, wanda ya haɗa da masu jari, masu hidima, lebura, etc. zaka iya kasancewa mai yin aiki a biya kawai ba tare da ka saka ko sisin kaba. 

                            kadan daga cikin ayyukan da zaka iya yi a biya ka a Digital marketing sune;

 1-Bude shufukan yanar gizo (creating website ).

2-Jagora ( referral)

3-Hada manhaja ( application development)

4- Saka Hotuna masu motsi (a YouTube)

5-Talla  (adds).

wannan kadan ne daga cikin ayyukan da ake samun kudi da su ta hanyar yanar gizo

A shiri na gaba zamu kawo muku cikakken bayani akan kowane daga cikin wadannan hanyoyi da muka zayyano a yau.

         Mun gode da sauran mu.


Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

MU KOYI COMPUTER

BASIC COMPUTER SYSTEM ll

HAUSA WEB SERVER